Hutu a duniya mara hutu

Hutu a duniya mara hutu

Takaitawa

Damuwa da yawan aiki suna kai mutane da yawa zuwa kabari kafin lokacinsu. Amma a cikin halitta, Allah ya tsara magani domin matsalar damuwa: a ranar hutu. An tsara wannan rana mai tsarki a matsayin albarka domin ’yan Adam su huta daga aikinsu kuma su kasance da lokaci tare da Allah. Abin takaici, duk da cewa Allah ya umarci mutane su tuna da ita, amma yawanci sun manta da wannan rana ta musamman, kuma da yawa sun manta da mahaliccin da ya ba su.

Nau'in

Ƙassida

Mawallafi

Sharing Hope Publications

Akwai a cikin

22 Harsuna

Shafuffuka

6

Saukewa

Mita Duran ta rasu. Mawallafiyar nan mai hazaka, yar shekara 24 daga Indonesiya ta fadi kan kujeranta. Menene ya faru? 

Mita ta yi aiki a kanfanin talar kasuwanci, inda bukatar aiwatar da aiki ke da yawa aikin kuma na da nauyi. Kamin mutuwarta, ta rubuta sako a zauren sadarwa na yanar gizo ta ce “daren yau kwana na takwas kenan ina rike da mabudin ofishi… Bani da rayuwa tawa.”

Ta dangana da wurin sosai, duk da bata samun barci. Ta dangana ne sosai akan ruwan lemun kwalba mai suna Krating Daeng wanda mun fi sani da Red Bull. Sakonta na karshe a yanar gizo shine “awowi 30 akan aiki har yanzu kuma ina da karfi.” A nan ne fa ta sume har ga mutuwa. 

Menene ya faru? Mita ta mutu saboda yawan aiki.

Yau, yawancinmu na da aikace aikace da dama. Duniya a yau na karfafamu da mu kara kuzari wajen aiki, domin hanyoyin samun kudi su karu, sannan mu kara siyan ababan more rayuwa. Muna fama da gajiya, rashin barci da kuma rashin hutar da kwakwalwar mu. 

Watakila aiki bai daure mu kamar Mita Duran ba, amma rayuwa ta dora mana nauyi sosai. Ko wannan shine nufin Allah garemu? Shi mai bada salama ne. Sa’anda muka mallake hankulanmu da aiki, ko mukan sami salama? Wannan ba hakabane!

Idan muna fama da gajiya, babu shakka mukan manta da wani abinda Allah yace mu tuna. Bari mu duba abinda ya ce game da hutu. 

Danna alamar “dakata”

Allah mai rahamane mai jinkai kuma. Ya sani cewa bil’adama na bukatar karin karfin jiki da kuma karfin ruhaniya, kamar yadda ake yi wa wayar salula ko kuwa kwanfuta chaji. Saboda haka, annabi Musa ya rubuta dokar Allah:

Ka tuna da ranar asabat, ka kiyaye ta da tsarki. Kwana shida zaka yi dukan aikinka, amma rana ta bakwai asabat ne ga ubangiji Allanka. A cikinta ba za ka yi kowanne aiki ba (daga bangaren farko na littafi mai tsarki wanda aka sani da Attaura: Fitowa 20:8–10).

Wannan dokar Allah mara canzawa ta fadi mana cewa mu tuna da rana ta bakwai. A cewar wasu yaruka da dama na duniya sun amince da cewar wannan ranar ta bakwai ranar hutune wanda ake kira “Asabat.” Menene ya sa Allah ya umurcemu da mu tuna da ita? Ya san da cewa mantuwa damuwace ga mutane, tun farawa daga Adamu. Ba za mu manta da dokokin Allah ba, domin tawurin kiyaye dokokinsa ne kadai zamu tuna dashi mu kuma yi tafiya cikin tafarkinsa.

Amma menene ya sa Asabat ya zama rana na musamman? Allah ya fadi mana,

A cikin kwana shidda Ubangiji ya halici sama da kasa, teku, da mabulbular ruwaye da dukan abinda ke cikin su, ya kuma huta a rana ta bakwai. Ubangiji ya albarkaci ranar asabaci ya kuma tsarkake ta (Fitowa 20:11).

Asabaci matunaciyace cewar Allah ne mahalici. Wasu mutane sunyi gardamar cewa tunda Allah ba ya gajiya, ba zai bukaci hutu a rana ta bakwai ba. Amma Allah bai huta domin ya gaji bane; amma ya dakatar da aikin halitane domin ya kebe lokaci mai tsarki domin mu huta.

Allah ya ga cewa ranar hutu na da muhimminci ga bil’adama. Ya halici rana ta bakwai, Asabaci, ma’ana kebewa ko dakatar da aiki. Sabo da haka, rana ta bakwai ga kowace mako ranace ta musamman da ya dace mu danna alamar “dakatawa.” Za mu hutane daga dukkan aiki mara tsarki na rana guda daya domin tunawa da kuma yi masa sujada. 

Ko ba abin farinciki bane idan ubangidanka ya umurceka da ka kara samun hutu? Wannan shine dai dai abinda Allah ya umurta! Yabo ga Allah! Babu shakka shi mai rahamane! 

Kiyaye ranar ubangiji da tsarki

Ranar Asabat rana ce kebabbe ga dukan mutanen duniya domin su kiyaye ta da tsarki. An kiyaye wannan rana da tsarki a lokacin da mutane suka gaskanta da Allah daya tun kafin kafuwar Yahudawa, Kristoci, Musulmai, ko Hindu. An kuma dankawa mutane a lokacin da aka hallici duniya. Adamu da Hauwa’u sun kiyaye Asabat, kuma Allah bai taba umurtanmu da mu manta da abinda ya ce mu tuna ba. 

Amma abin takaici, an cika mantawa da Assabat. Annabawa sun yi gargadi ga Yahudawa da cewa Allah zai kawo hallaka a bisansu har muddin sun manta da Assabat. Basu ji gargadinsa ba, saboda haka aka rushe Urshalima, iyalensu kuma aka kai su bauta. Kristoci ma sun manta da Assabar ta wurin canza rana mai tsarki zuwa ranar Lahadi sabanin abinda Allah ya umurta. Musulmai suna ibadarsu ranar juma’a amma sun manta cewa dole sai mun huta akan ranar assabat domin cikakkiyar biyayya ga mahalici. 

Menene ya sa kamar dukkan duniya ta manta da wannan rana mai muhimminci? Ko akwai wani dalili na boye da ta kawo wannan mantuwar?

Yesu Almasihu ya yi mana gargadi akan mulkin duniya mai zuwa wanda shaitan (Shaytan) zai yi amfani dashi domin juya zukatar mu daga mahalici. Za a rinjayi miliyoyin mutane da su yi ibada a ranar Assabat na karya. Idan shaidan zai sa mu manta da ranar mahalici, yana da begen zamu manta da mahalicin da kansa. Amma, har idan mun kiyaye Assabat na gaskiya, muna nuna alamar kaskanci ga mahalicinmu kuma muji dadin kyautar hutu, nishadi da salama.

Shigowa cikin hutun Ubangiji

Annabi Musa ya rubuta cewa “Ubangiji ya albarkaci rana ta bakwai” (Farawa 2:3). Ka gaji kuma babu sauran karfi? Akwai albarku a cikin Assabat! 

Mita Duran, mawallafiya daga indonesiya, ta mutu ne sabili da yawan aiki—amma kada ka bari hakan ya faru da kai. Allah yana gayyatarka da ka huta daga dukan aiki a kowanne mako domin samun dandanon albarkar ranar Assabat. 

Idan kana son ka gane yadda Allah ke bamu hutu, salama, da warkaswa, a tuntubemu ta hanyar da aka rubuta a wannan mujjallar.

Copyright © 2023 by Sharing Hope Publications. Ana iya bugawa akuma rabar da wannan mujjalar ba tare da izini ba, idan dalilan ba na kasuwancine ba.
Anyi amfani da nasosi daga littafi mai tsarki cikin tsohuwar hausa a saukake. Copyright © 2003, 2004 from The Bible League. All Rights Reserved.

Yi rajista don samun wasikunmu

Kasance na farkon wanda zai san lokacin da sabbin littattafai ke samuwa!

newsletter-cover