
Ko kana bukatan mu’ujiza?
Takaitawa
Allah yana da dogon tarihi na ba da mu’ujizai ga mutanensa, a daidai lokacin da suke bukatarsu. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana labarai da yawa game da annabce-annabce da suka cika, da waɗanda aka warkar da su, da kuma abubuwa masu ban mamaki da za su iya zuwa domin amsa addu’a kawai. Wannan ƙasidar tana bada dalilai da yawa da yasa zamu iya gaskatawa da Littafi Mai-Tsarki a matsayin kalmar Allah da bata canzawa, da kuma yadda za ka iya kusanci da Allah don mu'ujizar ku.
Nau'in
Ƙassida
Mawallafi
Sharing Hope Publications
Akwai a cikin
21 Harsuna
Shafuffuka
6
A kwai wata zuriya na iyali da ke neman ingancin rayuwa, sai suka kudurta zasu yi hijira zuwa wata kasa. Tafiyar, bai kasance da sauki ba domin sun ketare hamada da kafa. Akwai macizai, kunamu, da zufa mai tsanani. Idan mutum na ciwo ko ya fadi da baya, yan bindiga sukan kai masa hari.
Ba da jumawaba abincinsu ya kare, amma shugabansu ya roki Allah ya yi abin al’ajibi. Washe gari da safe bayan sun falka daga barci, sai sun ga birbidin wami abu kamar na gurasa a kasa. Yana da dandano mai dadi, kamar an hada da zuma. Gashi kuma a yalwace yadda zai kosar da kowa! Sunyi kwanaki kamin su ketere hamadan, kuma kullum wannan gurasan na fadowa daga sama. Daukaka ga Allah, sun sami tsira!
Wannan labarin zai zama da ban mamaki, amma ya faru. Yana daya daga cikin al’ajibai da suka faru a cikin littafi mai tsarki wanda aka sani da attaura, Zabura, da Injila. Akwai daruruwan labarbaru na abubuwan al’ajibai da Allah ya aikata a rayuwar mutane. Wannan littafin na da muhimmanci a wannan zamani, domin mutane da yawa na bukatan mu’ujizai a rayuwarsu.
Mu’ujizai na wannan kwanaki
Acikin wannan kwanaki, munga yaki, tarzoma, faduwar tattalin arziki, rashin aiki cututtuka da kuma mutuwa. Bani da tabbas akan matsalarka a yanzu. Kila an koreka daga gidanka. Kila akwai wani naka wanda ke tsakanin rai da mutuwa. Kila kana kokarin samun aiki.
Ko da menene yanayinka, Allah ya damu da kai kuma zai iya aikata aikin al’ajibi yau kamar yadda ya aikata a baya. Sa’anda kana cikin bakinciki ka karanta littafi mai tsarki, littafin al’ajibi.
Kalmar Allah ga wannan zamani
Wadansu suna kiwuyan karanta littafi mai tsarki domin an taba gaya masu cewar an chanza wadansu ababa daga ciki. Kila wannan rashin fahimta na tasowane saboda da halin wadansu mabiyan littafi mai tsarki. Wadansu lokuta mukan ga mabiya addinin Krista suna shan giya, suna yin ca ca, suna sa kaya yadda bai dace ba, suna cin naman aladu, kuma basu kyautatawa mutane.
Gaskiyar shine littafi mai tsarki bai goyi bayan wadanan halaya ba. Idan Krista sunki yin biyayya ga kalmar Allah, wannan ba zai canza muhimmincin kalmomin ba. Annabi Ishaya ya rubuta, “ciyawa takan bushe, furanni kuwa suyi yaushi, amma kalmar Allah zai dauwama har matuka” (Ishaya 40:8). Ko kana ganin cewa mutane suna da ikon canza kalmar allah, koko suna batashi da munanan halayensu ne?
Littafi mai tsarki yayi magana akan annabi Dauda da mutanensa cewa sunyi tafiya da sandukin alkawari, babban akwatin zinare dake dauke da dokoki goma. Dokoki goman nan dokokine na Allah domin rayuwar tsarki an kuma rubutasu a duwatsune sannan aka saka a cikin akwatin zinare. Da suna kan tafiya, wani mutum yayi yunkurin taba wannan akwatin, nan take ya fadi mattace!
Idan Allah bai bar hannun mara tsarki ya taba wannan sandukin dake dauke da kalmarsa ba, ta yaya zai bar miyagun mutane su taba kalmarsa da almakashi ko alkalamin yin gyara? Allah yana da cikakken ikon kare kalmarsa.
Maganar gaskiya shine, littafi mai tsarki shine littafi mafi tabbas a duniya. Acikin kwanakin nan, wadansu makiyaya uku a Palestine—Muhammad edh-Dhib, Jum’a Muhammad, da Khalil Musa sun gano rubutattun kalmomin Allah wanda ya bata a tekun matacciyar teku (dead sea). Wannan babban tsintuwa ya bamu damar kwatanta littafi mai tsarki na yanzu da tsohon da aka rubuta a fata shekaru 2,000 (dubu biyu) da suka wuce. Wannan ya kasance da ban mamaki, wanda ya nuna cewa babu wanda zai iya canza wahayin Allah. Idan kana bukatan al’ajibi, kana da tabbacin cewa littafi mai tsarki abu ne wanda ya dace ka duba! Anan za ka samu labaru masu kayataswa kamar na annabi Nuhu, Ibrahim, Yusuf, Yunana, Daniel, Dauda, da Sulaimanu. Kila ka taba jin kadan daga cikin tarihinsu, amma littafi mai tsarki na kunshe da cikakken labaru akansu!
Zo ka sami al’ajibin ka
Ko da wace irin hargitsice ke rayuwarka, littafi mai tsarki na kunshe da labari domin ka:
Ko kai ko wani naka yana ciwo? Karanta labarin Na’aman, hafshan sojojin siriya mai ciwon kuturta.
Ko kana gwagwarmaya domin ciyar da iyalinka? Ka karanta game da gwamruwa wanda ta yi rayuwa a lokacin yunwa da karamin tandun mai da garin flawa wanda ya ki karewa.
Ko rayuwarka na cikin hatsari? Karanta game da Ebed-Melech, mutumin Habasha wanda ya kasance bawa a fadar sarki, wadda rayuwarsa ta sami tsira a lokacin yaki domin ya gaskanta da Allah.
Ko kana ganin kai bare ne? Ka karanta labarin Hajara daga kasar masar, wanda ta ga aikin al’ajibin Allah a lokacin da aka nuna mata kiyayya.
Ko matsalolin rayuwa na karya maka gwiwa? Ka karanta labarin Yesu Kristi wanda ya mika hannunsa abisa teku domin ya tsayar da hargitsin teku ya kuma ceci almajiransa daga hatsarin jirgin teku.
Amsar al’ajibi
Sa’anda mun karanta littafi mai tsarki, muna addu’a da gabagadin cewa mun sami biyan bukata. Yesu Kristi ya ce, “Dukan abinda kuka roka a cikin addu’a, ku gaskanta, za a baku” (Matta 21:22). Sa’anda mun karanta labarun wadanda Ubangiji ya yi masu aikin al’ajibi, zuciyar mu yakan sami karfafawa da begen kai rokon mu zuwa sama.
Ko kana bukatan mu’ujiza? Ka samun karfafawa da ayukan al’ajibai da ke cikin littafi mai tsarki ka kuma tambayi Allah ya baka naka. Tabbas zai ji addu’arka yau!
Idan kana son ka kara samun masaniya game da al’ajibai dake cikin littafi mai tsarki, ka tuntubemu a hanyar da aka rubuta a bayan wannan mujalar.
Anyi anfani da nasosi daga littafi mai tsarki cikin tsohuwar hausa a saukake. Haƙƙin mallaka © 2003, 2004 daga Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki. Duka Hakkoki.
Yi rajista don samun wasikunmu
Kasance na farkon wanda zai san lokacin da sabbin littattafai ke samuwa!

Ka Sami Masu Sauraronka
Fitattun wallafe-wallafe
© 2023 Sharing Hope Publications