Yadda za ka yi tunani wa kanka

Yadda za ka yi tunani wa kanka

Takaitawa

Annabawan Allah sun yi annabci game da ikon addini mai haɗari da aka kwatanta da sunan “Babila.” In ji annabci, wannan ikon zai yi ƙoƙari ya tilastamu kuma ya ruɗe mu zuwa bautar ƙarya. Hanya daya tilo da zamu sami tsira itace tawurin yin tunani da kanmu da kuma cigaba da biyayya ga Kalmar Allah da ta bayyana. Wannan ƙasidar tana gaya mana yadda zamu yi amfani da hankalinmu domin mu zama masu hikima, masu tunani a lokacin rikicin duniya.

Nau'in

Ƙassida

Mawallafi

Sharing Hope Publications

Akwai a cikin

21 Harsuna

Shafuffuka

6

Saukewa

Ayanzu muka kammala hawa bisan dutsen Gunung Datuk. Sai na zauna tare da sabon abokina, Adzak, muna duban yanayin harabar. Ba da jumawaba, hirarmu ya koma kan addini.

“Ni mai yancin tunani ne” inji Adzak. “Ina da nawa duban a game da duniya.”

“Babu shakka,” na amsa. “Na sha jin matasa da yawa a kasar maleshiya suna cewa su masu yancin tunani ne su.”

Adzak yayi dariya. “Ya dace mu yi tunani da kanmu. Ashe akwai rikicewa, idan ba haka ba, wannan zai sa ka haukace.”

“Amma idan mun koma gida fa?” Na yi tambaya. “Anan Maleshiya, yawancin matasa suna kiran kansu masu yancin tunani, amma a gida ana sa mana ido domin mu dinga yin adinin Musulunci ko Buddi. Me kake gayawa iyayenka?”

“Ba na gaya masu,” inji Adzak. “Ina yin abinda suke so. Zan iya yin tunani wa kaina, amma ba zan gayawa kowa ba.”

Ko yancin tunani na da muhimmanci?

A wadansu bangarorin duniya, gaskantawa da abinda bai dace ba na iya kai ga a kori mutum daga al’umma, a koreshi a wurin aiki ko a kashe mutun. Yin tunani wa kanka yana iya zama da hatsari. Amma yana da muhimmanci? 

Duniyarmu na cike da ra’ayoyi masu kyau da kuma munana. Domin a tace masu kyau daga munana sai anyi tunani da kuma tattaunawa akansu. Idan ka sayi wani abu mai tsada—kamar zinare, safron ko babbar wayar salula, ba biya kadai za ka yi ka kai gida kawai ba. Sai ka duba da kyau domin ka tantance ka kuma tabbatar da cewa ka sayi mai kyau sosai. Haka ya kamata mu aiwatar da ra’ayoyinmu. 

Akwai rikicewa da rudu da yawa a duniya, wannan kuma yakan kara muni idan wadansu sun tilasta ra’ayoyinsu akan al’umma. Bari in gaya maka game da wani muhimmin annabci. A wani tsohon littafi wanda ake kira “bayyanuwar Yesu Kristi,” wannan annabcin ya yi bayani akan wadansu mutane da su ka yi kokarin tilasta rudaddiyar ra’ayin addininsu akan wadansu. Yana cewa “fadaddiya ce Babila babba, domin ta sa dukan kasashe sun sha daga ruwan anab na hasalar fasikancinta” (Ruya ta Yohanna 14:8).

Wadannan kalmomi na alamu basu da wuyan ganewa. Babila sananniyar tsohuwar birnice, amma ma’anar sunanta shine “rudu.” Wannan birnin “fadaddiya ce” ba domin ruduntaba amma domin ba ta so ta bar rudunta. Ta rinjayar da kasashen duniya da su bi ruhun fasikancinta ta hanyan hautsana ibada ta gaskiya da karya. Wadannan ra’ayoyin karyan sun sami karbuwa. Wannan annabci game da “Babila” na misaltan wata bangaren ruhaniya ta duniya wadanda suka yi na’am da karya sa’anan kuma daga bisani za su tilastawa wadanda suke bin gaskiya domin su bi ra'ayinsu na karya.

Annabcin Yesu Kristi ya bayyana cewa wadannan abubuwa zasu faru a kwanakinmu. Ba shakka kana ganin hakan yana kan faruwa. Ko akwai wadanda suke misaltan Allah da ra’ayoyi na karya? Ko ka taba nuna rashin gamsuwa a lamirinka?

Na’am, shi ya sa yancin tunani da kanka yana da muhimmanci.

Yadda za ka yi tunani wa kanka

Wadansu basu da matsala wajen bin addinin al’ummansu. Basu yin tunani game da abinda suka gaskanta. Suna bin al’adun addinin da bashi da ma’ana ko kuma ya cutar da mutane. Wadansu lokuta, shugabanen addinai, da ya kamata su nuna mana hanyar Ubangiji, suna cike da ayukan rashawa da cin hanci.

Ta yaya zamu sami gaskiya? Ina mai ra’ayin mu gaskanta annabawa. Don me? Akwai dalilai guda uku:

  1. (Daya) Annabawa sun bayyana masaniya game da rayuwan nan gaba. Annabi Daniel yayi anabcin fankama na tarihin nahiyar turai da yin mulkin mallaka a duniya. Yesu Kristi (Isa al-masih) yayi annabcin rushe urushalima a alab 70 bayan mutuwarsa. Annabi Musa yayi harsashe game da tarihin Isma’ila da karshen zamani.

  2. (Biyu) Annabawan sun bayyana nasara na kimiya da kuma sani na fanin kiwon lafiya. Annabi Musa da ya yi rayuwa shekaru 3,500 da suka wuce, ya yi nasiha game da ware masu cuta da ke yaduwa, zubar da datti da kuma tsabtace na’urori aikin asibiti. Ya ware dabbobi tsakanin masu tsabta da marasa tsabta. Kazalika yace kada mu ci jini ko kitsen dabbobi masu tsabta. Harwayau, wadanda suke bin wannan shawaran kiwon lafiyan suna samun karin shekaru 15 fiye da sauran jama’a.

  3. (Uku) Allah yana amsa addu’o’in wadanda suka gaskanta gareshi da annabawansa. 

Rubutun annabawa suna cike da bishewa—amma kafin mu amfana da su, sai munyi tunani mai zurfi, mu gwada bangaskiyarmu mu kuma duba yanayin imaninmu. Tunani abune mai kyau a bangaren addini.

Yanzu, menene yakan faru sa’ilinda muka nemi masaniya game da abinda ba daidai bane? Ya kan zama kamar gaskiya daga fari. Amma sa’anda muka fara niman gaskiya, mukan fara ganin matsaloli da wannan shawara. 

Gaskiyace kadai makarin karya. Ba a rasa komai idan anyi bincike da kyau. Sa’anda mun kara yin bincike, gaskiya yakan kara bayyana. 

Mummunai, yakamata su kasance masu hikima a duniya, domin Allah yana bishemu da hikimarsa. Idan ka iske kanka a inda ba za ka iya yin tunani ko tambayoyi a sake ba, toh babu shakka wannan ba daga wurin Allah bane. Allah yana gayyatan dubawarmu saboda gaskiya tana da kuzarin tsaya bincike. Amma Babila tana kwadaitar da karya sannan ta kulle kwakwalwanmu domin hana mu tunani mai zurfi.

Idan kana cikin rudu sannan kana tunani cewa kana Babila, toh ka fito daga cikinta! Dawo gefen Allah domin samun basira. Yi tunani da kanka sa’anan kayi tambayoyin da suka dace. Baza’a bashe ka ba. 

Ko kana son karin masaniya game da bayanuwar Yesu Kristi? A tuntubemu ta hanyoyin da aka rubuta a bayan wannan mujjalar.

Copyright © 2023 by Sharing Hope Publications. Ana iya bugawa akuma rabar da wannan mujjalar ba tare da izini ba, idan dalilain ba na kasuwancine ba.
Anyi anfani da nasosi daga littafi mai tsarki cikin tsohuwar hausa a saukake. Haƙƙin mallaka © 2003, 2004 daga Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki. Duka Hakkoki.

Yi rajista don samun wasikunmu

Kasance na farkon wanda zai san lokacin da sabbin littattafai ke samuwa!

newsletter-cover