
Niman Rahama
Takaitawa
Yaya kamanin rahamar Allah take? Shin ko yakan ce “Na gafarta muku” ne kawai, ko kuwa Yana tanadar da hanyar share ayukan kunyan da muka aikata? Wannan ƙasidar tana ba da labari na asali domin taimakawa wajen bayyana ma'anar sadaukarwar. Masu karatu zasu sami bege don sanin cewa za’a iya gafarta musu zunubansu da kuma kawar da kunyarsu.
Nau'in
Ƙassida
Mawallafi
Sharing Hope Publications
Akwai a cikin
21 Harsuna
Shafuffuka
6
Fatima tana zaman kadaici alokacin bukin sallar idin-Adha, zafin kadaicinta ya fi karfin jimriyarta. Zaman kadaicinta laifinta ne ko ba haka ba?
Fatima ta tuna yadda takan rika yin musu sosai da mahaifinta akan auren Ahmed. Tana cikin kuruciya da kuma kauna. Ta yaya mahaifinta zai ce babu? lokocin da ta gudu daga gida ta auri Ahmed, mahaifinta ya ce kada ta kara taka Kafanta a gidanshi.
A tunaninta, zata iya Jimrewa Kunyan da zata fuskanta saboda kaunar da take yi wa Ahmed. Amma ba da jimawaba, ta amince da cewar mahaifinta yana kan gaskiya. Ahmed ba mutumin da ta zata tana kaunarsa bane. Ya barta ya koma wa wata macen.
Fatima ta ji kunyar kanta. Ta gaskanta cewar ta gamu da adalci sannan kuma tana cika nata gurbi. Ta fahimci adalci sosai. Amma sai dai, zuciyarta yana bidan rahama.
Madaukaki mai rahama da jinkai
Idan zamu fadi gaskiya, dukan mu munyi kuskure mun ki jin muryar basira. Mun bata ma wasu rai. Wasu ma sun bata mana rai. Al'ummarmu mu na cike da mutane masu yin kurakurai. Gafartawa kanmu da kuma wadansu babu sauki!
Ko akwai rahama ga kurakuranmu?
Ka yi tunani ko sau nawane ka maimaita wannan furuci “bismillah Al-Rahman Al-Raheem”—“acikin sunnan Allah, mai rahama, mai jinkai.” Menene muhimmincin rahama?
Ba mamaki saboda al’ummarmu—da kuma zukatanmu—na bukatar rahama sosai.
Rahama: Hanya mafi inganci
Wasu shekaru da suka wuce, wani mai suna Abdul-Rahman yayi fada har ya kashe makwabcinsa Kareem. Rayuwa ya zama da kunci ga wadannan iyalai a wannan karamar kauye a kasar masar. Iyalen Kareem sun bukaci ramuko, sannan Iyalen Abdul-Rahman suna kare shi saboda tsoro. Abdul-Rahman baya son rayuwar ramuko ya cigaba. Sai ya bukaci shawara daga wurin shuwagabanin kauyen, sunce masa ya yi al’adar likkafani.
Abdul-Rahman sai ya kawo farin likkafani ya dibiya wuka akai. Sai ya je ya sadu da iyalen Kareem a kasuwa, sa’ilinda dukan mutanen kauyen ke kallonsa. Sai Abdul-Rahman ya durkusa a gaban Habib, kanin mamacin, ya mika masa likkafanin da wukan. Sai ya bukaci rahama da sasantawa.
Habib ya sanya wukar a bisa wuyan Abdul-Rahman. Shuwagabanin kauyen suka kawo yar tunkiya, Habib zai dauki kuduri: yayi gafara ko kuwa ramako? Sa’anda ya dibiya wukar a wuyar abdul-Rahman, ayukansa sun bayyana, “yanzu ina da iko. Kowa yana kallo; kowa kuma ya san ina da yancin kisa da kuma damar aikata hakan. Amma na zabi rahama da sulhu. Zan kawo ga karshen, dadaddiyar gabar jini.”
Ya kauce daga Abdul-Rahman sannan ya yanka yar tunkiya. Sa’anda zafi da haushin daukar fansa ya hushe akan dabban, Habib ya rungumi Abdul-Rahman. Salama tsakanin iyalennan guda biyu ya dawo.
Idan bil’adama zasu iya samun daman hada adalci da rahama, babu shakka Allah yana iya yin hakan ma.
Yesu Almasihu: Rahama daga Allah
A inane za mu iya koyan rahamar Allah? Yana da sauki. Ba mamaki ka taba ji cewa Yesu almasihu (wanda aka sani da Isa Al-Masih) ana kiransa “rahama” daga Allah. Wannan na nunin cewa yana rike da cikakkiyar rahama. Hanyoyinsa, koyaswarsa a cikin bishara, wanda aka sani da linjila—wannan shine hanyar gafara da sasantawa.
Yesu almasihu zai iya cika wannan gurbi saboda shi kadaine mara zunubi wanda Allah ya aiko. Kowane annabi da dan sako mai tsarki na bukatan gafara saboda kurakurai, amma banda Yesu almasihu. An fyauce shi zuwa aljannah a maimakon ya jira ranar shari’a saboda bai taba yin kuskure ba—koda karamace.
Saboda wannan daliline yasa ake kiransa rahamar Allah. Ya nuna mana kwatancin rahama mai tsarki ya kuma koyar da yadda za a iya samun rahamar Allah.
Ta yayane Yesu almasihu zai iya taimakona?
Yana rubuce da cewar Yohana mai baptisma (wanda aka sani da Yahaya) ya hangi Yesu almasihu a cikin taron jama’a, sai aka nuna masa wahayi daga wurin Allah, da kakkausar murya yace “gashi! Dan ragon Allah wanda ke dauke da dukkan zunuban duniya!” (Bishara, Yohana 1:29). Yesu almasihu shine kamar ragon da ya kawo hanyar sulhu ga Abdul-Rahman.
Idan an hukumtamu saboda laifin da muka aikata, wannan shine adalci. Amma Yesu almasihu, wanda bai kasance da zunubi ba, ya dauki wannan gurbin saboda kurakuren mu. Babu wanda ya tilasta masa. Shi da kansa ya dauki mutuwa saboda cika gurbin da adalci ke bukata. Shine mutun mara aibi wanda ya taba rayuwa, amma ya bada kansa aka mayas da shi kamar rago a labarin Abdul-Rahman. Shi yasa bayan ya wahala saboda mu, Allah ya dauke shi zuwa aljanna.
Babu mamaki kila akwai hargitsi a rayuwarka. Kila ke kamar Fatima ce wanda masoyinta yayi watsi da ita. Kila wani ya taba tsananta maka abaya, ko kuma antaba bata maka suna. Kila kai kamar Abdul-Rahman ne mai laifi sannan kana tsoron ramako.
Yesu almasihu zai iya taimakawa. Za ka iya yin gajeruwar roko kamar haka:
Ya ubangiji, ba zan iya biyan zunubaina ba. Amma na san ka turo Yesu almasihu kamar rahamarka zuwa garemu. Ka gafarceni saboda ayukansa kyawawa da ya yi saboda yan Adam. Ka taimakeni domin in fahimci hanyoyin Yesu almasihu saboda in sami dandanon rahamarka a rayuwata. Amin.
Idan kana bukatar samun naka bisharar, ka neme mu a hanyoyin da aka rubuta a wannan mujallar.
Copyright © 2023 by Sharing Hope Publications. Ana iya bugawa akuma rabar da wannan mujjalar ba tare da izini ba, Idan dalilan ba na kasuwancine ba.Anyi anfani da nasosi daga littafi mai tsarki cikin tsohuwar hausa a saukake. Haƙƙin mallaka © 2003, 2004 daga Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki. Duka Hakkoki.
Yi rajista don samun wasikunmu
Kasance na farkon wanda zai san lokacin da sabbin littattafai ke samuwa!

Ka Sami Masu Sauraronka
Fitattun wallafe-wallafe
© 2023 Sharing Hope Publications