
Tsaro daga miyagun ruhohi
Takaitawa
Mugayen ruhohi suna da ƙarfi, amma ba su da ƙarfi kamar Yesu Almasihu. Wannan ƙasidar ta kwatanta yadda Yesu ya fitar da aljanu daga mutane masu wahala kuma ya taimaka musu su sami warkarwa. Hakanan shi zai iya yi mana a yau. Littafinsa yana koya mana duk abinda ya kamata mu sani don mu kuɓuta daga fitina da zalunci. Har ila yau, yana koya mana yadda za mu guje wa yaudara da masu ruɗin aljanu kafin ya dawo.
Nau'in
Ƙassida
Mawallafi
Sharing Hope Publications
Akwai a cikin
21 Harsuna
Shafuffuka
6
Aljannu suna ko ina. Ko ka kirasu ruhohi, fatalwa, ko aljannu, su na da ban tsoro. Bokaye da masu duba suna da yawa, amma ko za su iya karemu?
Zan ba ka sirri guda uku game da miyagun ruhohi domin samun kariya, ka kuma daina jin tsoronsu.
Kariya daga miyagun ruhohi
Wani mutum yana tube tsirara yana kwalla ihu. Ya na da aljannu da yawa, kuma babu wanda zai iya taimaka masa. Mutanen kauyen sunyi kokarin daurashi da tsarka, amma yakan tsinkasu da karfi fiye da na mutane, sannan ya gudu ya koma makabarta da zama. Ya dauki Kwanaki da yawa yana kuka da kuma yanka kansa da duwatsu.
Sa’anda wani mai suna Yesu Kristi wanda aka sani da Isa al-Masihu ya iso.
Mutumin yana da tulin aljannu da yawa, sa’anda ya bude bakinsa domin neman taimako, aljannun suka tsautawa Yesu cewa ka kyale mu. Amma Yesu bai rabu da su ba. Yana sane da abinda ke faruwa. A cikin rashin tsoro ya umurci aljannun da su rabu da mutumin.
Aljannun suka roka cewar “kada a kaimu cikin kiyama!” Suka roka a basu izini su shiga garken aladu. Yesu ya umurcesu da su bar mutumin su shiga cikin dabbobi mara sa tsabta. Nan take, mutumin ya dawo cikin hayacinsa, garken aladun kuma suka gudu zuwa bisan hayi inda akwai teku.
Daga bisani, mutumin ya sami yanci. Yayi godiya sosai! Amma wannan ba shi ne labarin kawai ba. Yesu Kristi yana da iko maigirma fiye da na miyagun ruhohi. Dukan inda ya je, yakan warkar da wadanda suke da aljannu. Ya ba mabiyansa iko a bisan miyagu:
Hakika, Na baku iko . . . abisa duka ikon magabci, babu abinda zai taba lafiyanku. Amma kada ku yi murna saboda wannan, domin ruhohi suna kalkashinku, amma kuyi farinciki domin sunayenku na rubuce acikin littafi a sama (daga bishara, wanda aka sani da Injeel, Luka 10:19, 20).
Sa’anda mun bi Yesu Kristi, zamu sami kariya a wannan rayuwa da kuma tabbacin rayuwa na nan gaba! Bari mu duba matakai uku domin samun yanci daga miyagun ruhohi.
Mataki na 1. (Daya): Kayi alfahari da ikon sunan Yesu Kristi
Mataki na farko shine ka bidi kariya a cikin sunan Yesu Kristi. Ta ikon kanmu, ba mu da wannan karfi. Amma idan munyi shelar sunan Yesu Kristi a rayuwanmu, miyagun ruhohi za su rasa karfinsu! Yesu yayi magana game da mabiyansa: “A cikin sunana zasu kau da ibilisai” (Bishara ta hannun, Markus 16:17).
Har Idan ka gaskanta da dukan zuciyarka cewa Yesu Kristi zai yantas da kai, hakan zai faru! Ka yi wannan roko mai sauki ga Allah, “Ubangiji, ka kubutad da ni daga miyagun ruhohi acikin sunan wanda ka aiko, Yesu Kristi!”
Mataki na 2 (Biyu): Ka bidi tsabtar ciki da waje
Yesu Kristi ya koyasda cewa kada mu ba miyagu dama. Yace, “Mai mulkin duniyannan yana zuwa, amma ba shi da komai aciki na” (Bisharar, Yohanna 14:30). Dole mu tsarkake kanmu daga rinjayar ibilis.
Menene ma’anar cewa ibilis “bashi da komai a cikin mu”? Ma’ana shine ba shi da komai acikin zukatanmu da gidajenmu wanda yake nashine. Dole mu zubar da guru da layu. Dole mu guji ayukan zunubi kamar batsa, shan kwayoyi da giya. Idan muna cikin masu tsafin magana da matattu ko yiwa wasu tsinuwa, dole mu daina yanzu. Mu tsabtace harabarmu daga harin shedanu. Sa’anan dole mu yi addu’a ga Allah ya gafarta mana ya kuma tsabtacemu daga ciki.
Mataki na 3 (Uku): Ka cika rayuwarka da haske
Bayan Yesu Kristi ya kubutad da kai daga ikon aljannu, ka gayyaceshi ya yi mulkin rayuwarka. Kada ka bar rayuwarka babu komai. Yesu Kristi yace,
Sa’anda mugun ruhu ya fita daga mutum, ya kan je busashiyar wuri domin neman inda zai huta, idan bai samu ba. anan zai ce “zan koma gidana daga inda na fito.” Sa’annan idan ya dawo ya samu wurin a tsabtace kuma a shirye. Nan zai gayyato wadansu ruhohi guda bakwai wanda suka fi shi mugunta domin su zauna tare; Yanayin wannan mutumin zai fi na farko (Bisharar, Matta 12:43–45).
Sa’anda an kubutad da kai daga aljannu, ka cike rayuwarka da hasken littafin Yesu Kristi, wato littafi mai tsarki. Yesu Kristi ya zo kamar “haske a cikin duniya, domin wanda ya gaskanta gareshi kada ya yi rayuwa cikin duhu” (Bisharar Yohanna 12:46). Ka nemi littafin Yesu Kristi ka dinga karantawa domin haskensa ya kori duhu waje.
Kariya domin gaba
Muna rayuwa a kwanakin karshe inda miyagun ruhohi suna aiki fiye da da. Yesu Kristi cewa ya yi, kamin ya dawo, miyagun ruhohi za su yi ayukan al’ajibi domin su rinjayo mutane da yawa. Ga wadunsu, aljannu na bayyana masu a sifar ban tsoro kamar fatalwa: wasu kuma suna bayyana masu kamar mala’iku ko yan’uwansu da sun rigaya sun mutu. Iblis da kansa zai yi kwaikwayon Yesu Kristi!
Amma kada ka bari karya ta rudeka. Idan ka bi Yesu Kristi, shi zai ba ka ikon gujewa iblis. Abokina, ko da menene kalubalenka a yau, bari Yesu Kristi ya yantas da kai!
Idan kanason mai bin Yesu Kristi ya yi maka addu’a domin samun yanci daga miyagun ruhohi, ka tuntubemu ta adireshi dake bayan wannan mujallar.
Copyright © 2023 by Sharing Hope Publications. Ana iya bugawa akuma rabar da wannan mujjalar ba tare da izini ba, idan dalilan ba na kasuwancine ba.Anyi anfani da nasosi daga littafi mai tsarki cikin tsohuwar hausa a saukake. Haƙƙin mallaka © 2003, 2004 daga Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki. Duka Hakkoki.
Yi rajista don samun wasikunmu
Kasance na farkon wanda zai san lokacin da sabbin littattafai ke samuwa!

Ka Sami Masu Sauraronka
Fitattun wallafe-wallafe
© 2023 Sharing Hope Publications