
Gabagadi a gaban shari’a
Takaitawa
Yin tunani game da ranar shari'a ya kan sa mutane da yawa a cikin tsoro. Ta yaya za mu kasance da tabbacin cewa za mu wuce lafiya a cikin wannan rana ta ƙarshe ta hisabi? Allah ya ce zai ba mu Lauya—Wani wanda zai yi mana roƙo a cikin shari’a kamar yadda lauya yake ɗaukan ƙararmu a kotun duniya. Wannan ƙasidar ta gabatar da mu ga wannan Lauyan kuma tana koya mana yadda za mu sami tabbaci yayin da muke tunanin hukunci mai zuwa.
Nau'in
Ƙassida
Mawallafi
Sharing Hope Publications
Akwai a cikin
21 Harsuna
Shafuffuka
6
Wata safiya, na bar masaukina zuwa wata ganawa mai muhinminci. Na makara saboda haka ina tuki da gudu—fiye da yadda aka ka’ida. Na yi rabin tafiya zuwa inda zani, sai dansanda ya tsayardani, cewa dole sai naje ofishinsu. Sai nasami karayan zuciya saboda na san ina da laifi.
Bayan da dansandannan ya bude mini takardan laifi, nan take aka sammace ni zuwa kotu. A nan, na hadu da wani abokina lawyer ma’aikaci a kotun. Yayi mamakin ganina. Sa’anda na yi masa bayanin matsalata, sai yace “kada ka damu. Zan wakilceka.” Sai na yi farinciki. Abokina zai kasance lauya na.
Domin abokina ya fito fili ya wakilceni, alkalin ya ci mani karamar tara. Na bar kotun ina godiya ga Allah.
Abin tsorone tsayawa gaban alkalin duniya. Amma wannan karamin abune idan an kwatanta da tsayawa a gaban Allah a ranar shari’a. Idan wannan ranan gobe ne, kana shirye?
Shiri domin shari’a
Wadansu mutane suna nuna halin shagwaba agame da shari’a. Suna shan giya da taba, chacha, zuwa gidajen kulub suna kuma kallon ayukan asha. Kila suna da masaniyar cewa ana rubuta ayukansu a littafin ajiya, amma suna kunshe a cikin yaudarar shaitan. Basu damu ba.
Wadansu suna amsawa da tsoro sosai. Lokocin ibada ba ta wucesu. Suna tunanin azaban kabari dana jaharnama sosai, har sun manta da kauna da kuma alherin Allah.
Amma kamar yadda na sami wakili a kotu, Allah ya tanadarmana da wakili wanda zai taimakemu a wurin shari’a. Ba lallai sai ka kasance kai kadai ba!
Wanene wakilinmu?
Samun wakili ba sabon akida bane. Kowane shekara, dubban mutane sukan kawo ziyara zuwa wurare a arewacin Afrika da Asiya. Mutane da yawa sukanyi addu’oi a kaburburan manya manyan shugabane domin su wakilcesu.
Yana da kyau mu ba wadannan shugabanen girma, amma yin addu’a da bidan kariyarsu haramun ne. Sun riga sun mutu ba kuwa zasu iya yin maka komai ba. Annabawa ma suna cikn kaburburansu, suna jiran ranar tashin mattatu.
Kodashike haramun ne mu bukaci taimakon mattatu, amma bidar roko ba laifi bane. Amma wanene zai iya roko mana? Dole sai shi wanda
(Daya) Yake araye (domin mattatu bazasu iya yin magana a madadinmu ba).
(Biyu) Mara zunubi (saboda wanda doka ta kasheshi ba zai iya wakiltan wadansu ba).
Wanene zai iya cika wannan gurbin? Babu wani illa kaunataccen Yesu Kristi, Isa al-Masihu, wanda yake a raye a sama kuma bashi da aibi.
Yi tunani akan wannan—ko akwai wani wanda zai iya cewa bashi da zunubi? Adamu ya ci daga haramtaccen yayan itace, Nuhu ya bugu da maye, Ibrahim ya yi karya, Musa ya kashe mutum; Dauda ya kwace matan wani. Ba za ka taba samun wani annabi wanda bai taba yin kuskure ba ko ya roki gafara ba.
Amma Yesu Kristi bai taba yin zunubi ba. Shi da kansa yace “wanda ya aikoni yana tare da ni. . . domin akulum ina aikata abinda ya gamsheshi” (daga bishara, wanda akasani da linjila, Yohana 8:29).
Fuskantar shari’a da salama
Yesu Kristi yana raye a sama kuma bashi da zunubi. Yana shirye domin ya wakilce ni da kai. Kuma zai sake dawowa ba da jumawaba.
Idan zai sake dawowa zuwa na biyu, wannan ya nuna cewa Yesu Kristi shine annabi na karshe. Fiye da annabi—shine wakilinmu, shugaba da salama a ranar shari’a. Ya gaya mana, “Hakika anafada maku . . . dukan wanda ya kiyaye kalmomina ba zai taba ganin mutuwa ba” (Bishara ta hannun, Yohana 8:51).
Yesu ba mattace bane; yana raye! Kuma yana gina al’ummansa anan duniya ko yanzu. Wadansu lokuta yana gayyatan mutune zuwa rukuninsa tawurin mafalki ya bayyana kansa da farin tufafi ko tawurin yin aikin al’ajibi sa’anda muka yi addu’a a cikin sunansa.
Ko kanason ka sami salama a ranar shari’a? Ka furta bangaskiyarka a cikin Yesu Kristi. Don me zamu kallaba bangaskiyarmu a kan wadanda sun mutu kuma basu san abinda zai faru a ranar shari’a ba? Yesu yana da tabbacin makomarsa a aljannah. Kamar abokina da ya wakilceni a kotu, zai taimake mu.
Ko kana shakkan cewa wannan abun mamakin ba zai kasance gaskiya ba. Yesu Kristi yace, “idan kun roki komai a cikin sunana, ni zan yi” (Bishara ta hannun Yohana 14:14). Ka jarraba domin sanin idan abinda ina fada maka ko gaskiya ne. Idan Yesu zai iya biyan bukatunmu yanzu, babu shakka zamu iya gaskantawa ya zama wakilinmu. Ka yi addu’a a cikin sunan Yesu da zuciya daya za ka ga abinda zai faru. Za ka iya yin addu’a ka ce:
Ya Allah, inason in sani tabbas idan Yesune shiryayyen wakilinmu a ranar shari’a. Idan wannan gaskiyane, ka amsa addu’ata (Ambaci suna a nan). Na yi wannan roko a cikin sunan Yesu Kristi. Amin.
Idan kana da bukatar sani akan yadda zaka bi Yesu Kristi, nememu tawurin bayanin dake wannan mujjalar.
Copyright © 2023 by Sharing Hope Publications. Ana iya bugawa akuma rabar da wannan mujjalar ba tare da izini ba, idan dalilan ba na kasuwancine ba.Anyi anfani da nasosi daga littafi mai tsarki cikin tsohuwar hausa a saukake. Haƙƙin mallaka © 2003, 2004 daga Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki. Duka Hakkoki.
Yi rajista don samun wasikunmu
Kasance na farkon wanda zai san lokacin da sabbin littattafai ke samuwa!

Ka Sami Masu Sauraronka
Fitattun wallafe-wallafe
© 2023 Sharing Hope Publications