
Gayyatar hijira!
Takaitawa
Ko kana marmarin wuri mafi kyau? Wurin aminci, farin ciki, da hutawa? Muna marmarin abin da duniya ba za ta iya bayarwa ba domin kowannenmu an halicce mu ne don Aljanna. Yesu Almasihu ya riga ya tafi can. Ya san hanyar, kuma a gaskiya, Ya kira kansa “hanyar!” Wannan ƙasidar ta kwatanta gaskiya masu muhimmanci game da Yesu da ke taimaka mana mu yi shiri don zama yan ƙasa a Aljanna.
Nau'in
Ƙassida
Mawallafi
Sharing Hope Publications
Akwai a cikin
21 Harsuna
Shafuffuka
6
Abdul-Malek gajiyayyen tsoho ne. Bayan rasuwar matarsa da yaransa, ya bar iraqi domin gujewa daga mayakan ISIS. Yanzu yana rayuwa shi kadai a urdun kamar dan gudun hijira.
Amma a can an sami alamar bege. Ya na da dan’uwa a kanada wanda ya yi albishirin samar masa aiki. Cike da farin ciki sai ya fara nemam bisa na shigan kasan domin samun rayuwa mai sauki. Bayan shekaru da yawa, an bashi izinin shigan kasar kanada. Abdul-Malek ya cike da murna!
Amma kash murnarsa ba ta dauwamaba. Bayan ya isa kanada, ya gane cewa rayuwa bayan hijira babu sauki. Kullun yana kan aiki. Ga makwabtansa sun cika surutu. Gane yanayin sifirin motocin haya da wahala take balle ace ma harshen turancinsu!
Abdul-Malek yayi burin zuwa wuri mafi kyau, amma bayan isar sa, zuciyarsa ba ta cinma buriba. Sai ya fara tunanin ko zai iya cika wannan burin a wani wuri dabam a duniya—ko dai ya jira sai yaje aljannah!
Hijira zuwa aljannah
Ko ka taba samun kanka a yanayin Abdul-Malek? Wannan burin zuwa wuri mafi daidaita yana kunshe a cikin zuciyar kowane mutum sannan zuwa aljannah ne gidan mu na asali zai cike wannan gurbi. Wannan buri zai cika ba da jumamawa ba! Alamu suna bayyanuwa a idanunmu, kuma wannan duniya yana kawowa ga karshe.
Shekaru da dama, litattafan Yahudawa, Krista, da Musulunci na bayyana inda “hijirarmu” daga wannan duniya zuwa wata take. Dukan wadannan addinai suna nuna cewa akwai mai ceto wanda zai cike wannan alamu.
Abin alfahari shine, wannan mai-ceton a adinin Krista da Musulunci ba wani bane illa Yesu Kristi wanda aka sani da Isa-almasihu. Shine mai ceto a lokacin da ya yi rayuwa a falastin, amma yana aljannah na tsawon shekaru 2,000 (dubu biyu) da suka wuce. Daga bisani zai dawo a ranar karshe domin shari’a.
Dawowan Yesu Kristi bayyananne ne a littafi mai tsarki, amma Musulmai sun gaskanta cewan zai sake dawowa, tunda an rubuta acikin qur’ani: “sa’anan shi (Yesu Kristi) zai zama alamar sa’ar shari’a, domin haka kada ka yi shakkan shari’a amma ka bi ni, wannan shine hanya tabbatacciya” (Az-Zukhuruf 43:61).
Kamar yadda ma’aikaci a ofishin shiga da ficewa kan ba da sharruda domin samun takardar bisa, Yesu Kristi yana gayyatarmu da mu kula da wadannan alamu domin sanin hanyar gaskiya zuwa aljannah.
Menene Yesu yace game da aljannah?
An rubuta a Bishara wanda aka sani da linjila cewa “zan je domin in shirya maku wuri. Idan na shirya maku wuri, zan dawo in karbeku zuwa wurina; domin inda nake, nan ku ma za ku kasance” (Bishara tahannun Yohanna 14:2, 3). Yesu Kristi yace zai iya kaimu aljannah!
Ya kuma bamu misalin abinda ke aljannah. Ya ce
Babu mutuwa kuma, bakinciki, kuka ko azaba ba (Ruya ta Yohanna 21:4).
Zamu samu gidaje masu gwanin kyau (Yohanna 14:2).
Maza da mata za su sami martaba da yanci iri daya (Galatiyawa 3:28).
Yana cike da haske, rahama da farin ciki (Ruya ta Yohanna 21:21–25).
Tabbas, wannan wuri shine muradin zuciyarmu!
Sa’anda Yesu Kristi zai dawo zuwa na biyu
Amma Allah ya aiko annabawa da yawa da yan sako masu tsarki. Menene yasa Yesu Kristi zai dawo zuwa na biyu? Wannan tambaya na da saukin amsawa idan munyi amfani da misalin hijira. Domin samun takardar yancin hijira babu sauki, mutane da yawa sukan dauki hayan lauyan hijira wanda ya san ka’idojin. Idan muna da jagora, tabbas zai taimakemu.
Hakannan, Yesu Kristi ne kadai ya yi bayyanuwa na biyu domin shine kadai ya san hanyan zuwa aljannah. Shi da kansa yace, “Nine hanya, Nine gaskiya, Nine rai” (Yohanna 14:6).
Dukan annabawa da yan sako da Allah ya aiko sunyi kuskure sun kuma nemi tuba. Amma ba Yesu Kristi. Ya yi rayuwa mara zunubi na shekaru 33 (talatin da uku) a duniya. Wannan shi ya sa aka fyauce shi zuwa aljannah.
Ya kamata muyi koyi daga Yesu Kristi, mara zunubi domin musami masaniya game da abinda muke bukata kafin mu shiga aljannah. Wannan shine hanya kadai mafi dacewa. Abin godiya, zamu iya yin koyi daga littafinsa mai tsarki.
Shiri domin dawowan Yesu
Ko ba abin farinciki bane ka samu tabbacin hijirarka zuwa wuri mafi dacewa? Ana maka gayyata na kasancewa dan kasa na gagarumin mulkin Allah a aljannah! Ba da jumawaba Yesu Kristi zai dawo domin ya kai mu wannan kaunataciyar wuri.
Ko yana iya kasancewa kana bibiyan mutane wanda basu san makomarsu ba a ranar gobe kiyama? Idan kana tare da Yesu Kristi, babu damar yin shakka. Ka roki Allah ya bisheka a tsayayyar hanyar Yesu Kristi. Kana iya yin roko kamar haka:
Ya Allah, zuciyata ta dade tana niman wuri mafi dacewa. Ka fid da ni da kaunatattu na daga wannan duniya mai wuya. Na gaskanta babu lokaci. Ka jagorance ni domin in shiga wannan wuri wanda ka shirya domin na. Amin.
Idan kana bukatar cikakkiyar littafin bishara linjila, ka nememu a adireshin da ke bayan wannan mujalar.
Fassaran Qur'ani zuwa Turanci na Yusif Ali.Copyright © 2023 by Sharing Hope Publications. Ana iya bugawa akuma rabar da wannan mujjalar ba tare da izini ba, idan dalilan ba na kasuwancine ba.Anyi anfani da nasosi daga littafi mai tsarki cikin tsohuwar hausa a saukake. Haƙƙin mallaka © 2003, 2004 daga Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki. Duka Hakkoki.
Yi rajista don samun wasikunmu
Kasance na farkon wanda zai san lokacin da sabbin littattafai ke samuwa!

Ka Sami Masu Sauraronka
Fitattun wallafe-wallafe
© 2023 Sharing Hope Publications